Jama’a Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Kalli Yanda Dandazon Matasa suka bi Shekh Bello Yabo Har Gidansa Suna Jinjina Masa Kan Fadin Gaskiya akan Zaluncin da suka ce Gwamnatin tarayya ta na yi akan ‘yan kasa.
Shehin Malamin Bello Yabo ya fito da sanyin safiya zai tafi uzuririnsa sai yayi kicibis da wasu dandazon matasa a kofar gidansa wadanda suka yi fitar dango takanas-takano suka ziyarce ahi domin jinjina masa da nuna masa lallai ana tare a harkan da’awansa, da kuma yanda ya kasance yana fadin ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari gaskiya komai dacinta.
An hango Matasan suna ta kokarin mika ma malamin wasu makudan kudade, amma dai Shehin Malamin ya ki karba, duk da ya yi farin ciki da wannan ziyara da suka kawo masa.
Ku kalli bidiyon a kasa:
Allah ya kara ma Malam lafiya. Allah ya kareshi da dukkan sharri, Allah kuma yasa gaskiyar da yake fedewa ta shiga kunnuwan wadanda ake fada mawa suyi aiki da ita.