Gidan Badamasi wani sabon fim ne na barkwanci da ake yi tsakanin wasu yara masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi.
Alhaji Badamasi hamshakin attajiri ne dan kimanin shekara saba’in ya taba yin aure a rayuwarsa, inda yake da ‘ya’ya da dama, wasu ma bai san inda suke ba a yanzu.
A cikin wannan wasan kwaikwayo, abin ya fara ta’azzara ne tun daga lokacin da Alhaji Badamasi ya kasa cika alkawarin da ya yi wa ‘ya’yansa na kudi. Yaki ya barke tsakanin uban marowaci da dan kwadayi.
Ba a taba yin fim irin gidan Badamasi a kasar ba. Fim ne na barkwanci wanda yake nishadantarwa da ilmantarwa ta hanyar amfani da hazikan ‘yan wasan barkwanci ta yadda mutum zai ci gaba da kallo yana jiran ya ga abin da zai faru nan gaba.